ASIWAJU BOLA AHMAD TINUBU
ASIWAJU BOLA AHMAD TINUBU

An ayyana dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023.


Sakamakon da Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Mahmood Yakubu ya karanta, Tinubu ya samu kuri’u 8,794,726 inda ya kayar da abokan hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da Peter Obi na Labour. Party, LP wanda ya samu 6,984, 520 da 6,101,533 bi da bi.

KWANKWASO

RABIU MUSA KWANKWASO

Rabiu Kwankwaso na jam'iyyar New Nigerian Peoples Party, NNPP, ya samu kuri'u 1,496,687, yayin da jam'iyyun siyasa suka hada kuri'u 666,298.