PDP ,LP,  sun zargi INEC da yin magudi a sakamakon zabe

PDP ,LP,  sun zargi INEC da yin magudi a sakamakon zabe



Jam’iyyun siyasa uku sun zargi hukumar zabe mai zaman kanta da yin magudi a zaben shugaban kasar da aka yi a ranar Asabar, saboda rashin sanyawa a shafinta na sakamakon zabe.


Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa an yi wannan zarge-zargen ne a wani taron manema labarai kai tsaye da jam’iyyun PDP, PDP, Labour Party da Action Democratic Party suka gudanar.


A cewar shugaban jam’iyyar LP, Julius Abure shugaban INEC, Yakubu Mahmood ya yi magudi a zaben.

Ya kira Mahmood yayi murabus.


“Sakamakon da INEC ta sanar ya nuna babban bambamci tsakanin wakilan jam’iyyarmu da ‘yan Najeriya da ke sa ido a rumfunan zabe.


“Kin kin bin tsarin zaben da INEC ta yi ya kawo cikas ga sahihancin zaben.


"Saboda haka, muna bayyana cewa INEC ta yi sulhu a zaben kafin a fara tattara sakamakon zabe," in ji shi.

MUN GODE DA ZIYARTAR SHAFINMU