Rayuwarmu Cike Take Da Kyawawan Abokai Nagari Amma Tabbas
Acikinsu Akwai munafukan abokan da sharrinsu yafi na sanannun makiya ganewa
tana da wahala amma wani zubin gane wane yana munafurtarka zaifi haka wahala
musamman idan kunkasan ce tare tsawon lakaci.
Kukasance damu acikin shafinnan namu domin sananr daku abu shida da idan abokinka yanayi to tabbas munafurtar ka yake.
Bukatar yin karya domin sukasance tare dakai dakuma sawa karaina kanka kakuma raina matsayinka.
Domin abokinka nagaskiya zaizauna dakai batareda samaka damuwa saikaka kara matsayinka ba kokuma yasakayin weani abu da bakai niyyaba.
2. Yin gulma da tsegumi.
Akwai wani abu dayake kan kwaryar munafuki shine sanyin gulmar abokansa aduk sanda kuka hadu.
3. Samuwar sharadi a abotarku.
·
Shin abokin ka still zaikasance dakai alokacin
daka rasa wani abu daka mallaka?
·
Shin zaicigaba da sonka ko dakwa kadaina yimasa
abunda kake yi masa?
·
Shin yanatare dakai ne saboda kai kanka badan
wani abu daka mallakaba?
·
Koyana zama dakaine saboda gudun mawar da kake
bashi?
Yakamata kazauna kayiwa kanka alkalanci muna fukan abokai
suna zauna dakai ne kawai alokacin da suke morarka amma aduk sanda sukaga babu
abun da suke samu agurin to alokacinne zaka neme su karasa.
4. Nuna sonkai..
Yana da kyau mutu yaso kansa idan baka sokan kaba wazakaso amma su munafukai suna nuna son kansune zuwa next level hartakankai da wani lokacin basa iys boyewa kuma yanada matukar wuya suyi wani abu wanda zai amfane ka.
5. Kishi da nuna bakinciki..
basuna nuna bakin ciki bane akan kudin ka bane kokuma taimakon dakaiwa wani suna bakin ciki ne akan nasara da daukakar da kake samu yanayi musu matukar wahala wajen tayaka murna ko kuma nuna farin ciki akan wani abu da ka samu.
6. Rashin yafiya.
Sunagani saurin laifinka da surin nuna bacin rai yayin da kayi musu kuskure suna kuma yayata kuskuren da kayi musu sannan kuma basa manta laifin dakayi musu zuwa tsawon lokaci.
Abubuwa shida kenan da muna fukan abokaine
kawai sukeyi bayan sanin hakan abun daya kamata muyi shine nuna taka tsantsan akan
wanda yake nuna mana wasu daga cikin alamomin nan bawai muyanke alakar mu dashi
ba allah yatai make mu da samun abokai nagari.
